15 Maris 2015 - 11:09
MILLOLI DA AQEEDU Kashi na 3

Na Shaik Hamzah Muhammad Lawal FA’IDA TA BIYU(2)

Fa’ida ta biyu itace bada fursa da kuma dama ga mutumin da yake ba Imamiyah yake yi ba ya saurara domin ya ji aqidun shi’ah daga mabubbuga wadda take amintata daga wurin yan shi’a wadanda suka yi karatu a wurin Malaman shi’ah,shukran la fakran ina so a nan in ce na yi karatu daidai gwargwado a wurin Hujjoji da Ayoyin Allah a cikin Aqidan shi’ah wannan zai iya Ahhalani ya bani dama ya zama ina magana da suldani akan shi’anci akan asasin abin da nake hikaitowa daga wadannan Hujjoji da Ayoyin Allah din wadanda da yawa yawan su suna da rai a yanzu saboda haka idan kana so ka san shi’ah alhalin kai ba dan shi’ah bane to wannan silsilan bahasin za taimaka yayi amfani amma da sharuddan da zan ambata insha Allahu a gaba in na zo ina so in yi magana akan sharuddan muhawara saboda muhawara tana da sharudda masu yawan gasken gaske wadanda in daya daga cikin wadannan sharuddan ya rushe to gaba daya muhawara ba ta da amfani saboda haka duk wadannan shimfida ne ba mu shiga cikin bahasin ba.Sannan bayan mun fadi sharuddan muhawara zamu fadi manhaj din da zamu bi a bahasin namu,wannan kuma shine muke nufi da Ilmi Acadeemiy saboda akwai abin da ake ce ma muhawara da akwai kuma abin da ake ce ma Munazarah,sannan akwai abin da ake ce ma Mujadala wanda kuma kowanne yana da ma’anar shi.To lokacin da mu ka zo za mu yi bayani akan sharuddan muhawara zan yi bayani akan wannan nuqda ta biyu.Ala kulli hal fa’ida ta biyu itace cewa wannan wata dama ce ga mutumin da yake da zuciya kubutatta wanda yake so ya fahimci shi’anci.Sabani a cikin yan Adam wannan la budda minhu ne wato dole ne a ringa samun sabani domin dan Adam tun lokacin da aka halicce shi har zuwa lokacin da Allah zai gaji kasa da wanda yake akan ta haka dan adam zai kasance yana sabawa.Annabawa ma an aiko su ne saboda warware sabani saboda haka mutane suna sabawa tun farkon al’ummar musulmi an saba,sahabbai ma akan kansu sun saba, Abubakar da Umar sun saba kamar yadda yake a cikin Sahihul Bukari kila zamu gani wata rana,sannan sahabbai sun saba da Manzon Allah{saw} wanda muke ganin bai kamace su su saba da shi ba,kuma shima ya fadi haka.Amma duk da haka sabani ya faru. Saboda haka sabani wani abu ne daya lizimci dan Adam amma yafi kamata ya zama cewa muna bincike ne akan mas’aloli a lokacin da muka samu Iktilaf ba lokacin da muka samu Kilaf kawai ba,wato har a lokacin da muke da bambamci ba a lokacin da muka saba kawai ba,mutane sun dauka kullun dole ne ya zama ana muhawara in aka saba,a’a, ana yin muhawara ma har a lokacin da ake da bambamci ina so in fahimci ra’ayin ka kuma akwai muhawarori masu yawan gasken gaske a cikin Al’qur ani wanda Allah{T} ya hikaito,alal hakika ma Alkur’ani ya hikaito ko ya yalwata ma’anar Hiwar inda ya fitar dashi daga da’iran Jidal ya shigar dashi da’iran tattaunawa. Tattaunawa ma Alkur’ani ya kira ta muhawara saboda haka wanan itace fa’ida ta biyu. Ita fa’ida ta biyu itace ba wanda yake so ya fahimci shi’anci dama akan ya karanta ya gani yanda shi’anci yake daga Malaman shi’a.Kuma anan muna so mu ce in mutum yana so yayi bincike akan Aqidun da bata shi ba to abu biyu yake bukata:- 1,Na farko shine ya dinka bibiyan wadanda ake ce ma A’alam a wannan Aqidan. 2,Na biyu kuma ya dinga bibiyan abinda yake mashhur(abubuwan da suka shahara). Wannan sharudda ne masu tsadan gasken gaske wadanda kila a gaba zan yi bayanin wadannan kalmomin guda biyu kuma ba wai shi’ah kawai ba, kowace aqida aqida in kana so ka yi bincike a kanta, to ka nemi Ummuhatul kutub na ita wannan aqidan sannan ka ji daga A’alam na aqidan sai kuma ka dauki abin da yake Mashhur ba abin da yake Shaaz ba(wato bako) a cikin aqidan saboda kowace Aqida tana da manya manyan littafai wadanda suke sune maraajiih wato makoma na ita wannan makarantan ko Aqidan sannan kuma ya hada da jin sharhin da malaman makarantar suka yi a wannan makarantar.kada mutum ya zo da kaifiyan shi yace zai fahimce ta da kanshi,wannan zan kara bayani kila a gaba.Kuma dole ya zama cewa yana bibiyan ra’ayoyin A’alaam na ita makarantar da yake so ya fahimta,amma a nan muna bayani ne akan A’alam na shi’ah ne. Abin da ake ce ma A’alaam sune kwatankwacin Ummuhatul kutub a bangaren mutane,wato kenan sune malamai fitattu shahararru wadanda suke iya yin bincike a ita makarantan har su kai inda zasu iya bada ra’ayi akai kuma dukkan wadanda suke wannan makarantar sun masu sheda akan su fitattu ne.Kowace makaranta tana da irin wadannan A’alaam din kamar in ka na so ka san ra’ayin As-salafiyyah maslan,kana bukatan mutum kamar Shaikul-islam Ahmad ibn Abdulhamid ibn Taimiya Al-harrani domin yana da littafai masu yawa misali:-akwai As- salihul Masnun Ala Shatimir Rasul,sannan akwai shahararren littafinsa wanda ake ce ma Minhajus Sunnatin Nabawiyyah Fi Naqdi Kalamish Shiati Wal Qadriyyah.To kana buqatan shi Ibn Taimiyyah sannan kuma kana bukatan littafan shi saboda littafan shi marja’ai ne a sanin ra’ayin salafanci.Sannan shi akan kanshi shi alami ne shine ma alami mafi fice a ita wannan makarantar wato shine Al-munazzimur Rasmi a wannan makarantar.Sannan in a yau ne kana ka na so ka san ra’ayoyi da Aqidun wahabiya ko Salafiya kana bukatan ka san wani mutum da ake ce ma Ash- shaik Abdullah ibn Abdul-Aziz bn Baaz,ba ka wadatuwa daga barin shi in dai da gaske kana so ka san ra’ayin wannan makarantar ne yana da rubuce rubuce masu yawan gaske,wasu na asali shi yayi su wasu kuma tahqiq yayi,yana da abin da ake ce ma Majmu’ul fataawa,sannan yana da ta’aliqi akan Fat’hul Bari na Ibn Hajar Al’asqalani domin ya karanta shi a matsayin tahqiq da tas’hih wato tas’hihan wa tahqiqan.Ka ga kana bukatan ka san ra’ayoyin shi akan Fat’hul Bari na bn Hajar Asqalani.Sannan ka na bukatan ka san malamin da ake ce ma shi Al- allamah Muhammad Nasirud-dini Albani shima yana da littafai masu yawan gaske shi ma a makarantar Salafiyyah ko Aqidan salafiyyah,Yana da littafin da ake ce ma Silsilatul Ahadithil sahihah wa Shai’un Min Fiqhuha wa Fada’iluha sannan ya na da akasin wannan littafin (muqabil) wato Silsilatul Ahadithil Da’ifah,Yana kuma da abin da yake ce ma Sahih At-tirmiziy da kuma Ibn majah.A nan wurin za ka ji ra’ayoyin shi masu yawan gaske.Sannan kana bukatar wani mutum wanda ake ce ma shi Dr Shu’aibu Al-ar’uuq wanda babban malami ne a Salafiyan yau,yana da rubuce rubuce masu yawan gaske da Tahqiqaat masu yawan gaske akan littafai.Kamar a ce Dabaqatul Hanabilah masalan,sannan kana buqatar kasan mutum wanda ake ce ma shi Dr Muhammad Rashid Sale,sannan kana buqatar ka san mutumin da ake ce ma Abdurrahaman ibn Suleiman Al-usaimim wadannan suna daga cikin A’alaam na makarantar.Ka ga baka wadatuwa daga barin su wadannan malaman idan kana so ka san aqidan wannan makarantar ma’ana ba ka buqatuwa daga barin su,to irin wadannan su muke nufi da A’aalam.A cikin shi’ah ma akwai A’alam na shi’ah,manya manyan maraji’ai wadanda suke duniyan shi’ah tayi i’itirafi da su akan cewa in suka yi magana suna fadin ra’ayi ne a cikin shi’a,to irin wadannan su kake buqata ba mutanen kan titi ba kuma ba mawaka ba sannan ba kowa da kowa ba,A’alaam na shi’ah kake bukata. Sannan kuma kana bukatan abu na uku da muka fadi shine ya zama cewa ka na bibiyan ra’ayin da yake Mash’hur a cikin ita makarantar.Kamar a salafiyyah za ka bibbiyi me wadancan malaman suka ce?Me ya shahara a tsakankanin wadancan malaman? Haka kuma in kana so kasan ra’ayin Ash’arawa kana bukatan kasan ra’ayin Abul-hasanul Ash’ari da kan shi da kuma wadanda suka yi intima’i zuwa ga makarantar,kamar irin su Abubakar Albaqillani.Ida n kuma kana so kai bincike akan Mu’utazila kana bukatan kasan ra’ayin Qaadil qudat Abduljabbar da wadanda suke a dabaqa din shi. Haka ake sanin ra’ayi a mazhaba ya dan uwa ba kowanne man habba wa dabba ba,kamar yadda kaji wadannan to a cikin shi’a ma haka ne sannan kuma sai ka bi abin da yake mashhur wato abin da ya shahara ba abin da yake ya zama ya kadaita ba,abinda shaaz. Kullum ka dinga bibiyan mashhur in dai ba kana bibiyan fitina bane,kasan akwai wadanda kur’ani yayi magana akansu cewa su kullun suna bibiyan Matashabaha minhu a kur’ani,mutum yana iya bin abin da yake matashabaha yana bibiya ne Ibtiga’al- Fitnah wato domin neman fitna,to kada ka zama irinsu ka zama mai adalci da Insafi a cikin bincike akan kowace aqida aqida ko da ba taka bace. Saboda haka ka bibiyi me ya shahara a ciki sannan kuma kasan me ya shahara a shi’a itama in kana so ka yi magana akan ta,wannan kuma haka yake a kowace aqida ko makaranta haka ya kamata kayi.Kana bukatan ka iya bambamce wa tsakanin firqoqi da suke cikin gidan makaranta guda daya,ka da ka dauki ra’ayin wata firqa ka jingina shi ga wata firqa,kamar a cikin shi’ah bai dace ba ka dauki ra’ayin wadanda ake ce ma Al-waqifa ka dora akan firqan da ake ce ma Ash-shi’ah al-isna ashriya sannan uwa uba wa ya baka da ma ka dakko ra’ayin Gullat ka dora su akan Yan shi’ah?domin su gulat ba ma kirga su a cikin Yan shi’ah domin a kowace makaranta akwai Gulat(masu wuce gona da iri),kamar misali a cikin mazhaban Abu Hanifa akwai wadanda suke ganin Abu Hanifa yafi Manzon Allah {SAW} ilimi wal iyazu billah.Kaga wannan ba shine ra’ayi mashhur a cikin Hanafanci ba ai ko?,ta na iya yiwuwa ma ya zama su Hanafawan basu dauke su a matsayin cewa su Hanafawa bane saboda haka ala kulli halin abin da ake bukata kenan. Sannan in ka shigo cikin makaranta kana neman abubuwan da suke mashhur to abin da za ka yi shine ka dauki irin wadannan A’alam na kowanne dariqa ka kuma san mashayan shi.Mutakallim ne a cikin shi’a ko Arif ne a cikin shi’a ko kuma shi Faqihi ne a cikin shi’a?,ko kuma Mufassir ko lugawy.?Saboda kowanne daga cikin su akwai wani mumdalaq ko mimbari daya taho daga gare shi,saboda haka ra’ayoyi suna bambanta akan asasin mumdalaqat.Sannan ya kamata ka sani akan cewa shi Ikbari ne ko Akabari?ko kuma Usuuly ne?Akwai wasu daga cikin malaman shi’a ana ce masu Akbariyuun ko Ikbariyuun,mafi yawa daga cikin malaman hadisi wadanda suka rubuta hadisan mu Akbariyuun ne.Sannan akwai wasu malamai da ake ce masu Usuliyuun wadanda su sun yi imani ne da dabbaqa qa’idoji a wurin tsamo hukunci a cikin shari’a.Akbariyuun bi dabi’atil hal kamar yanda sunan yakei shara zuwa gare shi sun tafi ne zuwa ga dogaro kacokaf zuwa ga hadisi a wurin daukan matsaya a kowani abu ko a kowace mas’ala mas’ala,sun yi kama da wadanda ake ce masu Ahlul hadis a cikin sunnah ko wahabiyawa ko salaf,su ba ruwan su da mazhaba. Saboda haka dole ka sani shin wannan malamin da kake saurare shi Akbari ne ko Usuliy?.Mu anan wurin muna tafiya ne akan bangaren malaman da suke su Usuliyun ne, sannan banda wannan kana bukatar kasan cewa daga wacce makaran ta ya taho?ta Najab ko ta Qum? asalin malaminshi shine Al-mirzah Na’iniy koko Shaik Abdulkarim Ha’iry.? Wannan majmu’a na ma’alumat din za su taimake ka a wurin shakkasa ko haddade da iyakance fahimta da iyakance abin da yake rubutawa sannan ka iya hukunci akai saboda haka ba karamin aiki bane wannan. Ya kamata kasan cewaYan shi’a suna nan tun farkon musulunci kamar yadda zamu tabbatar nan gaba insha Allah,kai da musulunci aka haifi shi’a,da shi’a aka haifi musulunci a ra’ayin mu wato abu daya ne.Tunda ra’ayin shine cewa abu daya ne da shi’a da musulunci ba bambamci,kenan shianci wani abu ne wanda ya faro tun daga asali,ba abune wanda ya faro shekara hamsin ko shekara dari balle shekara arba’in ko talatin wanda suka wuce ba.Kenan kana bukatan aiki mai yawan gasken gaske kafin ka iya fadin ra’ayi akai.Kana bukatan ka zama babban malami ka zama Muqa’rin a cikin aqidu wato me yin muqaranan aqidu.To wadannan karatuttukan da za muyi muna cewa kila ya buda maka wasu irin tagogi dangane da wadannan Istilahohi da ra’ayoyin da muka fadi a yanzu domin zai baka fursa idan kana so ka sani.ABNA